1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HARIN BOMB A IRAQI

JAMILU SANIFebruary 2, 2004
https://p.dw.com/p/BvmA
A kasar Iraqi yau litinin aka baiyana cewa yan sari kanoken Iraqi sun harba wani gurneti ga wasu jerin motocin sojin Amurka,a dai dai lokacin da mukadashin sakataren tsaron Amurka Paul Wolfowitz ke ganawa da shugabanin riko na gwamnatin Iraqi a garin Mosul. Sanarwar data fito daga Brigrdiya janar Cater Ham. na sojin Amurka a kasar Iraqi,ta baiyana cewa masu kai harin na gurneti sun kaiwa motocin sojin Amurka hari ne,a lokacin da motocin na sojin Amurka ke tafiya a garin na Mosul,to sai dai kuma babu wani wanda ya sami rauni sakamakon kai wanan hari na kwantan bauna kann sojin na Amurka dake Iraqi. Da yake gudanar da ziyarar aiki a garin na Mosul,Mukadashin sakataren tsaron na Amurka ya kai ziyarar aiki wani ofishin yan sanda da kuma wani ginin kotu dake garin na Mosul. A jiya lahadi ne dai wasu yan kunar bakin wake suka kai wasu tagwayen hare haren bomb a garin Arbil na kurdawa dake arewacin Iraqi,inda wanan hali yayi sanadiyar mutuwar mutane 67,ciki kuwa har da manyan shugabanin kurdawa,a dai dai lokacin da ake gudanar da bukukuwa na Idi-al-Adha. Tagawagar sojin Amurka dake rufawa mukadashin sakataren tsaron Amurka baya,a ziyarar aikin yake gudanarwa a garin Mosul a yau litinin sun baiyana cewa mutane 67 suka rigamu gidan gaskiya yayin kuma da wasu 267 suka sami raunuka. Shugabanin kurdawan Iraqi,sun yi fatan cewa tagwayen hare haren boma boman da suka faru kann shugabanin kurdawa a garin Arbil,zai zamanto wani baban darasi da zai kuyawa bangaren na kurdawan Iraqi bukatar dake akwai ta kara hada kawunan su,ta yadda hakan zai samar da manufar data dace wajen jan ragamar mulkin Iraqi. Wani gidan talbijin din kurdawan Iraqi,ya bada labarin cewa wasu mutane biyu ne suka kai harin bomb din na jiya lahadi a garin na Arbil na kurdawa,sanye da wasu irin tufafi dake nuna cewa manyan maluman Islama ne,kuma daya daga cikin su ma har ya halarci bunkukuwan da aka gudanar da babar sallah a hedkwatar jama'iyar Kurdish Democratic Party ta KDP dake garin na Arbil na arewacin Iraqi. A yayin irin wadanan bukukuwa dai bisa al'ada ba kasafai jami'an tsaron ke gudanar da bincike kann bakin dake halartar bukukuwan na Iddi ba. Da misalin karfe 10.45 masu harin bomb din su biyu,suka kai wanan hari na bomb a dai dai lokacin da shugabanin kurdawa ke musabaha da juna don nuna murnar su ta an kamala salar iddi lafiya. Sanawar jami'an gwamnatin Amurka ta zargi yan sari kanoke na ketare ko kuma kungiyar ansarul Islam da kuma al-Qaeda da laifin kai hari kann kurdawan Iraqi,koda yake har yanzu babu wata kungiya data fito fili ta yi ikiraren kai harin bomb din na jiya lahadi a garin Arbil na arewacin Iraqin ba. Kantoman Amurka a kasar Iraqi Paul Bremer,yayi alkawarin yin aiki da jami'an tsaron Iraqi,wajen binciko mutane dake da hanun cikin wanan mumunan harin bomb da ya faru a jiya lahadi. Dr.Salah Abudulla daractan asibitin koyarwa na jami'ar birnin na Arbil,ya fada a yau litinin cewa mutane biyar daga cikin 58 da aka kwantar a asibiti sakamakon wanan harin bomb din na jiya lahadi sun rigamu gidan gaskiya.