1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bomb a birnin Riyadh

April 22, 2004

Gwamnatin Saudia ta ce zata dauki matakai na yaki da yan ta'ada.

https://p.dw.com/p/BvkO
Harin bomb a brinin Riyadh
Harin bomb a brinin RiyadhHoto: AP

Mahukuntan kasar Saudi Arabia sun fada a yau alhamis cewa zasu kara daukar tsauraran matakai na yaki da aiyukan yan tarzoma,tun bayan harin kunar bakin wake na kusa kusan nan da ya afku a birnin Riyadh wanda kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane hudu,yayin da wasu 145 kuma suka sami raunuka,to sai dai kuma wata kungiyar dake da alaka da kungiyar al-Qaeda ta ce ita ke da alhakin kai wanan hari.

Tun a jiya laraba ne dai wasu yan ta’ada suka dasa bomb cikin wata mota da nufin kaiwa wani ginen malakar gwamnati hari,kuma shine irinsa na farko tun bayan harin bomb din da ya afku a birnin Riyadh shekarar data gabata,wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 52 a lokacin da wasu yan ta’ada suka kai hari na kunar bakin wake wasu gidaje na zaman jama’a cikin watanin Mayu da kuma Nuwamba na shekarar data gabata.

Jami’an gwamnatin saudia,jaridu da kuma manyan maluman addini na kasar,sun nuna matukar damuwar su da halin da saudia ta sami kanta a ciki na hare haren ta'a’anci,don haka ne ma suka bukaci a hada karfi da karfe wajen yaki da masu kaiwa fadar gwamnatin ta saudia hari na ta’adanci.

Da yake magana da shugaban Palasdinawa yassar arafat ta wayar tarho bayan afkuwar harin bomb din birnin Riyadh na jiya laraba,yarima Abudulah bin Abdul Aziz mai jiran gado na saudia,ya shaidawa Arafata cewa mahukunta na saudia zasu dauki matakin da ya dace na murkushe aiyuka na yar tarzoma har sai an ga bayan su baki daya.

Da yake ziyartar wadanda wanan hadarin ya risa da su dake kwance a asibiti,ministan cikin gidan saudia Yarima Nayef bin Abdul Aziz ya baiyana cewa irin harin da yan ta’ada ke kaiwa jami’an tsaron saudia ya nuna a fili cewa tilas ne tilas ne hukumonin na Saudia suka hima wajen yaki da aiyukan tazoma.

A yau alhamis ne dai ministan cikin gidan na Saudia ya ganewa idonsa gawakin mutane uku daga cikin hudun da rasa rayukan su samakon harin bomb din da ya afku jiya a birnin Riyadh,wanda kuma suka hadar da wani kanal din dan sanda,wani maikacin gwamnati da kuma wata karamar yarinya yar asalin kasar Syria,wanda kuma hakan ya kawo adadin mutane 145 zuwa 148 da suka sami raunuka cikin harin bomb din da ya afku jiya a kasar ta saudia.

Jaridar Okaz ta saudia ta buga wasu labaru dake nuna cewa ba gaskiya bane a ce ana kai irin wadanan hare hare kann ne kann Amerikawa dake zaune a kasar ba,tun da shike wanan sabon harin da ya afku an kai shine kann yan asalin kasar ta Saudia.

A halin da ake ciki dai kungiyoyin dake da’awar kare muhiman wuararen ibada biyu da ake da su a kasar saudi Arabia sun sami nasarar kai harin da ya lalata hedkwatar jami’an tsaron saudia da aka dorawa alhakin yaki da aiyukan ta’ada,wace kuma ke karkashin maikatar cikin gidan saudia,kamar dai yadda wanan labarin ya fito daga wani sashin yanar giza gizo ta musulunci,ko kuma Islamic Website.

A makon da ya gabata ne dai gwamnatin Amurka ta umarci jami’anta na diplomaciya da su gagauta ficewa daga cikin kasar saudi Arabia a sabili da matsaloli na rashin tabas din harkokin tsaro a wanan kasa mai tsarki.