1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin boma-bomai ya kashe mutane 50 a Iraƙi

April 4, 2010

Iraƙi ta wayi gari cikin hare-haren boma-bomai a sassan birnin Bagadaza

https://p.dw.com/p/Mn2j
Hoto: AP

Motoci uku ɗauke da boma-bomai ne suka tarwatse a kusa da ofisoshin jakadancin Jamus, Masar da Iran a tsakiyar birnin Bagadaza. Kawo yanzu dai mutane 50 ne suka rasa rayukansu, baya ga wasu sama da 200 da suka raunana. Waɗannan tashin boma-bomai na kusan lokaci guda dai, sun auku ne bayan harin rokoki guda huɗu a daren jiya yankin Green Zone mai ingantaccen tsaro dake tsakiyar Bagadaza. Kazalika tashin wani bomb na gefen hanya ayayin shigewar motar sintirin 'yan sanda ya raunana  mutane 10. Jami'an Iraki dai sun danganta wadannan hare-hare da rashin sanin makomar ƙasar bayan zaɓen 'yan majalisa na ranar 7 ga watan maris. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yayi Allah wadan wadannan hare-hare akan hukumomin ketaren.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Abdullahi Tanko Bala