1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin boma bomai a birnin Algiers

Zainab A MohammedApril 11, 2007
https://p.dw.com/p/BvSu
Harin kunar bakin wake
Harin kunar bakin wakeHoto: AP

Harin kunar bakin wake ya kashe mutane da dama tare da raunana wasu, a headquatar ofishin prime ministan kasar Algeria,dake birnin Algiers a yau laraba.

Harin kunar bakin waken wanda aka aiwatar dashi ckin wata mota,ya haifar da rudadi a harabar ofishin prime ministan algeria Abdelaziz Belkhadem dama tituna dake kewaye.

Majiyar yansanda na nuni dacewa mutnae da dama ne suka rasa rayukansu wadanda suka hadar da shi mai kunar bakin waken,da kuma wasu jamian yansanda dake tsare kofofin shiga harabar premiern na Algeria dake tsakiyar fadar gwamnatin kasar dake Algiers.

Mr Belkhadem wanda ya tsallaka rijiya ta baya .ba tare da samun rauni a wannan hari ba,ya bayyana shi da kasance mugun nufi da mummanar akidar yan tarzoma.

Harin na yau dai ya huda tsakiyan ginin benen mai hawa shida ,inda ya tarwatsa tagogi da kofofi dama motoci dake tsaye acikin harabar.

Da farko na zata girgizar kasa akayi,inji lauya Tahar bin Taleb,yace mai dakina ta kirani tana kuka,nan take na ruga gida inda na tarar da tagogi a farfashe da sauran bangariri na ginin gidan.

Wannan harin boma bomai na yau dai na mai zama na farkon irinsa daya ritsa da birnin Algiers cikin shekaru masu yawan da suka gabata.

Majiya mai tushe daga fadar gwamnatin Algerian na nuni dacewa wasu hare haren kunar bakin waken ayau sun auku a wasu motoci guda uku a unguwar Bab Ezzouar,wanda ke kusa da filin saukan jiragen sama na kasa da kasa ,harin da ya lalata ginin ofishin yansanda ,tare da katse wutan lantarki a yankin baki daya.

Kawo yanzu dai jamian agaji na cigaba da kai dauki a headquatan ofishin prime ministan,ginin dake dauke da ofisoshin ministocin Algerian da dama.

A yan kwanakin nan ne dakarun gwamnatin Algeria suka kai somame akan mayakan sakai na Islama dake gunduwar Kabylie,kungiyar dake ikirarin kai mafi yawan munanan hare hare a kasar ta Algeria da wasu kasashe na ketare da suka hada da Tunisia.

A wannan somame dai akalla mayakasn sakan guda 20 da sojojin gwamnati guda 3 suka rasa rayukansu a wannan yanki.