Harin bama bamai a Iraqi | Siyasa | DW | 17.08.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Harin bama bamai a Iraqi

Dambarwar Siyasa da hare haraen bama bamai a kasar Iraqi

Hare haren bama bamai a birnin Bagadaza

Hare haren bama bamai a birnin Bagadaza

Alúmar kasar Iraqi sun wayi gari da fashewar wasu bama bamai uku da aka dasa a cikin wasu motoci a wata tashar mota dake lardin Al-Nahada. Wadannan bama bamai a cewar rahotanni sun fashe ne daya bayan daya cikin mintina goma a kuma dai dai lokacin da jamaá ke hada hadar tafiya wuraren aiki ko kuma neman kalace a safiyar yau. A kalla mutane kusan 50 ne suka rasa rayukan su nan take yayin da wasu mutanen fiye da 80 suka jikkata a sakamakon wadannan munanan hare hare kwanaki biyu bayan da yan siyasar kasar suka gaza cimma daidaito na sabanin raáyi akan sabon kundin tsarin mulkin kasar da ake gani zai taimaka wajen rage aukuwar tarzoma a kasar Iraqin, biyu daga cikin bama baman sun fashe ne a lardin Al-Nahada yayin da dayan kuma ya fashe a cikin wata mota a lardin Al-Kindi a cewar hukumomin lafiya a birnin Bagadaza. An ruga da wadanda suka jikkata zuwa asibitoci a birnin na Bagadaza.Yankin na Al-Nahada matattara ce ta motoci dake sadar da jamaá daga kudanci Iraqin zuwa birnin Bagadaza.

An baiyana cewa wadanda suka kai wadannan hare hare sun yi da niyyar yin mummunar Illa ga jamaá fararen hula domin a can baya yawancin hare haren yan sari ka noken sukan yi su ne akan jamián tsaro. A hannu guda dai kungiyar Al-Qaída ta bayar da gargadi a shafin ta na yanar Gizo inda take kashedi ga jamaár da suka yi yunkurin kada kuriár raba gardama a game da kundin tsarin mulkin Iraqin a watan Oktoba. Sabanin da aka samu a game da wasu batutuwa a kundin tsarin mulkin ya tilasta majalisar dokokin kasar ta kara waádin mako guda kwamitin rubuta kundin tsarin mulkin domin ya kammala aikin sa.

Wannan nan dai shi ne karo na karshe na waádin rubuta sabon kundin tsarin mulkin wanda hakan ke nufin cewa idan aka gaza cimma daidaito akan daftarin kundin tsarin mulkin, to babu makawa sai an rusa majalisar dokoki a gudanar da sabon zabe a cewar daya daga cikin wakilan kwamitin rubuta kundin tsarin mulkin Mukhtar al-Fadhal. P/M Iraqi Ibrahim al-Jaáfari da sauran yan siyasar kasar na sassauta batutuwan da suka hana ruwa gudu a game da rubuta kundin tsarin mulkin da cewa ya kamata a yi laákari da fadin kasar da kuma yanayin siyasar ta, yana mai cewa batutuwan da ake da sabanin raáyi akan su, ba matsaloli ne da zasu dauki tsawon lokaci na sasantawa ba, sai dai kuma yan siyasar na baiyana raáyin cewa banagarorin yan Sunni dana Shiá da kuma Kurdawa kowanne ya ja daga akan matsayin sa wanda ke nuna cewa har yanzu da sauran runa a kaba.

Akwai dai sabanin raáyi sosai a game batun rabon arzikin kasa da kuma ikon cin gashin kai daga bangaren kurdawa, daftarin kundin tsarin mulkin wanda zaá gudanar da kuriár jin raáyin jamaá akan sa a cikin watan Oktoba na daga cikin muhimman matakai na tafarkin siyasar kasar wadda Amurka da kawayen ta ke fatan zai share fagen janyewar sojojin su daga Iraqi. Jakadan Amurka a Iraqin Zalmay Khalizad wanda ya baiyana rashin jin dadin sa ga rashin cimma daidaito akan kundin tsarin mulkin ya kuma musanta cewa yawan sojojin Amurka da aka kashe tun bayan kawar da tsohon shugaban kasar Iraqi Saddam Hussaini ya rubanya yawan sojojin da suka rasa rayukan su a lokacin da sojojin taron dangin suka afkawa kasar tun da farko.