Harin bama bamai a Bagadaza | Labarai | DW | 12.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bama bamai a Bagadaza

Wasu jerin bama bamai masu karfi da suka face a tsakiyar birnin Bagadaza a yau din nan sun yi hallaka mutane fiye da 90. Bama baman wadanda aka dasa a cikin wasu kananan motoci guda uku sun tarwatsa wata kasuwa cike da jamaá tare da haddasa mummunan hasara. A waje kuma wani harin na kunar bakin wake ya kashe a kalla mutane tara. A daidai wannan lokaci a bara, yayin da ake bikin sabuwar shekarar musulunci wasu wadanda aka danganta da yan al-Qaída a Iraqi suka kai harin kunar bakin wake a kan masallacin yan shiá a birnin Samarra dake arewacin Bagadaza wanda haddasa zubar da jini a tsakanin mabiya dariku a birnin Bagadaza da sauran wurare a fadin kasar Iraqi. Munanan hare haren na yau sun auku ne a daidai lokacin da gwamnatin Iraqi ta yi kira da a gudanar da jimami na mintina goma sha biyar domin nuna alhini ga mutanen da suka rasa rayukan su a harin na Samarra.