Harin bama-bamai a Bagadaza ya halaka aƙalla mutane 75 | Labarai | DW | 22.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bama-bamai a Bagadaza ya halaka aƙalla mutane 75

Akalla mutane 75 sun rasu sannan sama da 150 sun samu raunuka sakamakon wasu tagwayen hare haren bam da aka kai da mota a wata kasuwar sayar da gwanjo dake tsakiyar birnin Bagadaza. Harin dai shi ne mafi muni tun bayan wasu tagwayen hare hare da aka kai a wajen harabar jami´ar Bagadaza wanda ya halaka mutane 70 kwanaki 6 da suka wuce. Wadannan tashe tashen hankula sun zo bayan isar rukunin farko na dakarun da shugaban Amirka GWB yayi alkawarin turawa a Iraqi. Sama da sojoji dubu 3 suka isa a Bagadaza don fara aiki a ranar daya ga watan fabrairu.