1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya kashe mutane 40 a Kabul.

Abdul-raheem Hassan
December 28, 2017

Harin ya faru ne a lokacin da mabiya shi'a ke bikin cika shekaru 38 da mamayar da Tarayyar Soviet ta yi wa kasar Afghanistan

https://p.dw.com/p/2q1zh
Afghanistan Anschlag in Kabul auf Afghan Voice
Hoto: Reuters/M. Ismail

Hukumomin birnin Kabul sun tabbatar da faruwar harin amma sun ce ana fargabar samun karuwar asarar rayuka sakamakon munin rauni da ya jikkata sama da mutane 30 baya ga mutane 40 da suka mutu nan take.

Babu wadanda da suka dauki alhakin kai harin kawo yanzu, amma kungiyar Taliban ta gaggauta nesanta kanta daga harin. Kabul na cikin wuraren da suka fi fuskantar munanan hare-hare a kasar Afaganistan bayan da Taliban suka sassauta hare hare amma kuma kungiyar IS ta ci gba da zafafa kai hare hare kan fararen hula da jami'an tsaro da kuma ma'aikatun gwamnati.

Wannan hari dai ya zo ne bayan da gwamnati ta karfafa matakan tsaro tun bayan wani mummunan harin bam da mota wanda ya kashe mutane 150 a kusa da ofisoshin jakadanci a watan Mayu.