1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya kashe dan jaridan AFP

Ramatu Garba Baba
April 30, 2018

Wasu tagwayen hare-haren bama bamai da aka kai a tsakiyar birnin Kabul na kasar Afghansitan sun halaka mutane 25 ciki har da wani dan jarida mai suna Shah Marai na kafar yada labaran Faransa AFP.

https://p.dw.com/p/2wtQk
Afghanistan Kabul Doppelanschlag
Hoto: Reuters/O. Sobhani

Babu tazara a tsakanin fashewar farko da ta biyu inji Dawood Amin, wani babban jami'in 'yan sandan birnin , ya kara da cewa Shah Marai dan jarida mai daukar hoto na kafar yada labaran Faransa AFP ya mutu ne a sanadiyar hari na biyun a yayin da ya ke tsakiyar aiki.  An dai shirya kai harin ne kan ginin da ake da tarin ofisoshi na kasashen ketare da ke yankin a cewar jami'in. Mutane sama da ashirin ne suka sami rauni a sanadiyar harin da ake zargin mayakan Taliban da kai wa a safiyar wannan Litinin.