Harin bam ya halaka akalla mutane 15 a birnin Basra | Labarai | DW | 03.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya halaka akalla mutane 15 a birnin Basra

Wani dan kunar bakin wake ya halaka akalla mutane 15 zuwa 21 aka sannan ya jiwa kimanin 80 rauni a wani harin bam da ya kai da mota a birnin Basra dake kudancin Iraqi. Wani dan sanda yace an kai harin ne cikin babbar kasuwar dake tsakiyar birnin. Yau dai kwanaki 3 kenan da FM Iraqi Nuri al-Maliki ya kafa dokar ta baci a birnin, inda aka shafe makonni ana zubar da jini tsakanin sojojin sa kai ´yan shi´a dake gwagwarmayar rike madafun iko tare da samun angizo a birnin. A kuma birni Bagadaza, an halaka wani ma´aikacin ofishin jakadancin Rasha sannan aka sace wasu jami´an diplomasiya su 4. ma´aikatar harkokin wajen Rasha a birnin Mosko da ma´aikatar cikin gidan Iraqi a birnin Bagadaza sun tabbatar da aukuwar wannan lamari. Rahotanni sun shaidar da cea wasu ´yan bindiga da ba´a gane su ba suka tsayar da motar ´yan diplomasiyar Rashan sannan daga bisani suka bude musu wuta.