1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam na mota a kanfanonin mai Fatakwal

December 18, 2006
https://p.dw.com/p/BuXN
Zaben Nijeriya
Zaben NijeriyaHoto: AP

A Naijeriya,an samu fashewar wasu abubuwa a harabar kanfanonin mai na Agip da Shell a birnin Fatakwal,amma babu wanda ya samu rauni.

Tun farko dai sai da kungiyar masu fafutukar yantar da yankin Naija Delta a Nigeria MEND cikin wani sako da ta aikawa kafofin yada labarai a yau ta yi barazanar dana bama bamai na cikin mota guda uku kowane lokaci daga yanzu.

Kungiyar wadda yanzu take garkuwa da wasu maaikatan mai 4 yan kasashen waje bata yi wani karin bayani ba cikin sakon nata.