1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam a wata makarata da ke Zariya

September 30, 2012

Tashin bam da harbe-harbe da safiyar Lahadin nan a wata makarantar addinin Islama a Zariya da ke arewacin Najeriya ya yi sanadiyyar rasuwar mutane biyu.

https://p.dw.com/p/16HmR
Smoke rises from the police headquarters as people run for safety in Nigeria's northern city of Kano January 20, 2012. At least six people were killed in a string of bomb blasts on Friday in Nigeria's second city Kano and the authorities imposed a curfew across the city, which has been plagued by an insurgency led by the Islamist sect Boko Haram. There was no immediate claim of responsibility for the apparently coordinated attacks. REUTERS/Stringer (NIGERIA - Tags: CRIME LAW CIVIL UNREST TPX IMAGES OF THE DAY)IL UNREST)
Hoto: Reuters

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin Yusha'u Shu'aibu, jami'in hukumar bada agajin gaggawa ta NEMa da ke Kaduna ya ce harin har wa yau ya yi sanadiyyar jikkatar mutane da dama.

Bam ɗin da ya tashi da harbe-harben sun faru ne a kusa da wata makaratar kwana ta addinin Islama mallakin sananen malamin addinin Islaman nan na Zariya Awwal Adam Albani.

Shaidun gani da ido sun bayyanawa manema labari cewar tashin bam ɗin ya yi sanadiyyar lalacewar wani bangare na makarnatar da kuma wasu gidaje da kusa da ita.

Kawo yanzu dai babu wanda ya ɗau alhakin kai harin. Harin dai na zuwa ne kwana guda kafin bikin ranar zagayowar cikar Najeriya shekaru hamsin da biyu da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Burtaniya, bikin da mahukuntan ƙasar su ka ce ƙwarya-ƙwarya za a yi lamarin da ya sa dama ke ganin cewa hakan na da nasaba da ƙalubalen tsaron da ƙasar ke fuskanta.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman