1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam a Turkiya.

Halimatu AbbasJune 8, 2010

Fashewar bam a kusa da wani asibiti ya jikata mutane 15 a Istanbul na Turkiya.

https://p.dw.com/p/NlHF
Inda bam ya tashi a IstanbulHoto: AP Photo

Mutane15 sun ji rauni a Istanbul, bayan fashewar wani bam a kusa da wani asibitin babban birnin na Turkiya. Kanfanin dillacin labaran ƙasar wato Anatolie ya ce bam ɗin ya tashi ne, a lokacin da motar sulke ta jami'an tsaro ke jagorantar jigilar ma' aikata. Babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakkin wannan harin.

Amma kuma harin ya zo ne a daidai lokacin da shugabannin ƙasashen Rasha da Iran da Syriya da kuma Afghanistan ke halartan taro kan harkokin tsaro da ke gudana a Istanbul. Babban birnin na Turkiya da ya ƙunshi mutane miliyon 18 ya saba fiskantar hare- haren ta addaci da ake ɗora alhakkinsu kan masu tsattsauran ra' ayin addini ko kuma Kungiyoyin 'yan tawayen ƙurdawa da ke neman dara ƙasar ta Turkiya gida biyu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu