Harin bam a kasar Iraqi ya halaka mutane da dama | Labarai | DW | 29.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam a kasar Iraqi ya halaka mutane da dama

Akalla mutane 25 sun rasu sannan kimanin 60 sun jikata a wani harin bam da aka kai da mota a tsakiyar wata kasuwa dake wani gari a kusa da birnin Baquba da ke arewa da birnin Bagadaza. An kai harin ne a garin Huwaider na mabiya darikar shi´a mai tazarar kilomita 60 arewa da Bagadaza, ´yan mintoci kalilan gabanin bude baki. Wani mai daukarwa kamfanin dillancin labarun AFP hoto a asibitin birnin Baquba inda aka kai da yawa daga cikin wadanda suka jikata, ya ce an shiga wani hali na yamutsi da rudu da hushi lokacin da ´yan´uwa ke neman karin bayani dangane da danginsu. A kuma garin Husaybah mutane 10 sun rasu a wani farmaki da dakarun Amirka suka kai kan wasu gine-gine da ake zargi mabuya ne ga ´yan tawaye. Sannan sojin Amirka 3 sun rasu a hare-haren da aka kai a Bagadaza da kuma Beishi. Sannan ´yan sandan Iraqi biyu sun rasu a fashewar wani bam a birnin Kirkuk.