Harin bam a birnin Beirut ya halaka mutane huɗu | Labarai | DW | 12.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam a birnin Beirut ya halaka mutane huɗu

Aƙalla mutane huɗu sun rasu sannan wasu bakwai sun samu raunuka a tashin wani bam a wani yanki dake kusa da fadar shugaban ƙasa dake wajen Beirut babban birnin ƙasar Lebanon, kamar yadda wata majiyar kungiyar agaji ta Red Cross ta faɗawa kamfanin dillancin labarun AFP. Bam din ya fashe ne lokacin da ake cikin hada-hadar zuwa aiki a unguwar Kiristoci ta Baabda dake kudu maso gabashin birnin na Beirut. Ɗaukacin ofisoshin jakadancin ƙasashen Larabawa da na yamma a wannan unguwa suke.