Harin bam a Bagadaza ya kashe akalla mutane 75 | Labarai | DW | 19.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam a Bagadaza ya kashe akalla mutane 75

Wani harin bam da aka kai da babbar mota a kan wani masalacin ´yan shi´a dake birnin Bagadaza ya halaka akalla mutane 75 yayin da sama da 100 suka jikata. Kamar yadda ´yan sanda suka nunar karfin fashewar bam din ya sa hayaki ya tirnike saman manyan gine gine a tsakiyar birnin na Bagadaza. An kai harin ne kwanaki biyu kacal bayan cikar wa´adin dokar hana fita da aka kafa a Bagadaza da zumar rage hauhawar tsamari da matakan daukar fansa bayan harin da aka kai kan wani masallacin ´yan shi´a dake birnin Samarra a makon da ya gabata. An yi musayar wuta jim kadan bayan fashewar bam din wanda ya auku a kusa da masallacin Khillani dake cikin unguwar hada-hadar kasuwanci ta Sinak. Limamin masallacin Sheik Saleh al-Hiidari ya ce an kai harin ne a daidai lokacin da jama´a ke barin masallacin bayan salllar azahar. Hakan ya faru ne a daidai lokacin da dakarun Amirka suka kaddamar da wani gagarumin farmaki akan ´yan al-Qaida a arewacin Bagadaza.