Harin 11 ga watan Satumba | Labarai | DW | 15.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin 11 ga watan Satumba

Wani wanda ake tuhuma da shirya makarkashiyar harin 11 ga watan Satumba a kan ƙasar Amurka Khalid Sheikh Mohammed ya amsa zargin da ake masa na jagorantar harin. Khalid Sheikh Mohammed ya amsa laifin ne a yayin zaman sauraron shariá da aka yi a keɓe a sansanin gwale gwalen Amurka dake Guantanamo a ƙasar Cuba. A jawabin sa Khalid Mohammed yace shi ne ke da alhakin dukkan farmakin da kuma sadarwa a tsakanin rassan ƙungiyoyin al-Qaída. Baki ɗaya dai Khalid Mohammed yace ya jagoranci shirya hare hare taáddanci guda 29 wanda ya haɗa da yunkurin Richard Reid na tarwatsa jirgin sama da kuma harin Bali na ƙasar Indonesia.