1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ƙunar baƙin wake a Pakistan

Wasu jerin hare-hare da 'yan Taliban suka ƙaddamar a birnin Lahore sun salwantar da rayukan mutane 31.

default

'Yan Taliban na Pakistan

Aƙalla mutane 31 sun rasa rayukansu a birnin Lahore na gabashin Pakistan, a lokacin da wasu 'yan ƙunar baƙin wake suka ƙaddamar da jerin hare-hare a wurin ibada na mabiya mazhabar Shi'a. Wasu ƙarin mutane 180 sun ji rauni bayan da waɗanda aka danganta da 'yan taliban suka tayar da bama-baman da ke jikinsu a cikin cunkoson jama'a da suka kai 35.000 da ke shirin yin buɗa baki.

Haren-haren ƙunar baƙin wake har 400, da suka salwantar da rayukan mutane 1.600 'yan Taliban suka ƙaddamar a ƙasar ta Pakistan cikin shekaru ukun nan da suka gabata. Suna zargin gwamantin Islamabad da mara wa Amirka baya a abin da suka kira yaƙi da addinin musulunci.

Ƙasar Amirka ta sanya ƙungiyar Taliban ta Pakistan a hukumance a cikin jerin ƙungiyoyin ta'adda da ta keman murkushe su. Wannan ƙungiya ta 'yan Taliban ta Pakistan, ta ɗauki alhakin harin da ya ci tura a dandali shaƙatawa na Times Squares da ke birnin New-York.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Halima Balaraba Abbas