Harin ƙunar baƙin wake a Iraƙi | Labarai | DW | 07.01.2008
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ƙunar baƙin wake a Iraƙi

Aƙalla mutane sha huɗu da su ka haɗa da shugaban wata ƙungiyar yan ta’adda sun rasa rayukansu wasu kuma su 25 sun jikata a tagwayen hare hare kunar baƙin wake da aka aiwatar a arewacin birnin Bagadaza. Wani ɗan ƙunar baƙin waƙe ya ta da bama bama da ya dɗaure a jikinsa ya auka wa shugaban majalisar wayar da kan al’uma Riyad al-Samaraey da magoya bayansa. Jim kaɗan bayan haka sai kuma wani ɗan ƙunar baƙin waƙe ya ta da bam daga wata mota da nufin auka wa motar dake kan hanyar zuwa asibiti da waɗanda suka samu raunuka
 • Kwanan wata 07.01.2008
 • Mawallafi Halimatu Abbas
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Clay
 • Kwanan wata 07.01.2008
 • Mawallafi Halimatu Abbas
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Clay