harin ƙunar baƙin wake a Kamaru
November 29, 2015Talla
Wasu mata ne guda biyu suka kai hare-haren a garin Dabanga da ke a yankin Arewa mai nisa na ƙasar.Gwamnan Yankin na arewa mai nisa Midjinyawa Bakary ya sanar da cewar ɗaya daga cikin matan,ta tayar da bam ɗin ne a cikin wani gidan iyalai, yayin da ɗaya ta tarwtsa kanta a cikin wani shago.
Ya zuwa yanzu ba a da masaniya dangane da waɗanda ke da alhakin kai harin. Sai dai ana kyautata zaton cewar Ƙungiyar Boko Haram ce ke da alhaki, saboda ta yi kaurin suna a wannan fanni.