Harim bom ya halaka rayuka a Iraki | Labarai | DW | 16.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harim bom ya halaka rayuka a Iraki

Mutane 40 sun halaka a wani harin bam mai muni a kudancin Bagadaza.

Rahotanni daga kasar Iraki na cewa akalla mutane 45 suka mutu a wani harin bom da ya auku a kasuwar tsoffin motoci a kudancin Bagadaza. Wani wakilin kamfanin dillancin labaran AFP na Faransa da ya shaida barnar da bom din ya yi, ya ce motoci da dama ne suka kone a wajen yayin kuma da a daya hannun sassan jikin mutane da kuma jini ke ta kwarara.

Wannan hari na wannan Alhamis dai, bayanai sun ce ya kasance hari mafi muni da ya kasance a yankin a bana, kamar yadda jami'an tsaron yankin suka tabbatar. Akwai ma wasu mutanen da aka yi kiyasin akalla 60 da suka ji munanan raunuka sakamakon harin. Ana kuma dora alhakin harin kan mayakan IS duk da cewa kungiyar bata ce komi ba, sai dai ta sha daukar alhakin irin wadannan hare-haren da ta saba kaddamarwa a kasar ta Iraki.