Hari ya rutsa da 'yan sanda a Afghanistan
June 30, 2016Talla
A cikin wani hari ne dai da aka kai wa ayyarin motoci 'yan sanda sabin dauka a wata unguwa mai cinkoson jama'a a da ke yammacin birnin na Kabul, 'yan sanda a kalla 27 suka mutu, tare da raunata wasu 40 a cewar wani jami'in ofishin ma'aikatar ministan cikin gidan kasar ta Afghanistan. Cikin wata sanarwa da ya fitar bayan harin, kakakin masu kai harin Zabihullah Mujahid, ya tabbatar cewa maharan na su sun kai hari ga motocin bus-bus guda biyu, kuma sun hallaka mutane da dama.
Shaidun gani da ido sun ce bayan tarwatsewar bam na farko, sai kuma ba da jimawa ba bam na biyu ya tashi a daidai lokacin da ake kokarin zuwa da sabin 'yan sandan wajen ayyukan horo.