Hari ya halaka mutane da dama a Pakistan | Labarai | DW | 27.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya halaka mutane da dama a Pakistan

Mutane da dama sun mutu sannan wasu suka jikata sakamakon wani harin kunar bakin wake a birnin Lahore na kasar Pakistan.

Wani harin kunar bakin wake da aka kaddamar a inda Kiristoci ke gudanar da bubukuwan Ista a birnin Lahore na Pakistan ya haddasa mutuwar kimanin mutane 60 yayin da wasu da dama suka jikata. Mahukuntan birnin sun nunar da cewar harin ya fi ritsawa da mata da yara kanana. Sannan wadanda suka samu rauni na cikin mawuyacin hali.

Wani dan takife ne ya tayar da bam da ke daure a jikansa a kofar shiga wurin shakatawa na Gulshane-Iqbal da ke Lahore ba tare da an san dalili ba. Ita kasar ta Pakistan ta saba fuskantar hare-hare ta'addanci daga masu kaifin kishin Islama. Amma har ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta fito fili ta dauki alhakin wannan harin.