1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari ya girgiza Tiripoli

Usman Shehu UsmanSeptember 8, 2016

Wannan harin ta'addancin dai an kai shi ne kusa da ofisoshin gwamnati ciki kuwa har da ofishin shugaban wushin gadi da kuma ma'aiktar harkokin wajen kasar.

https://p.dw.com/p/1JyR1
Anschlag auf Geheimdienst-Offizier in Bengasi
Hoto: Reuters

Rahotanni sun bayyana cewa wasu tagwayen bama-bamai ne suka tashi a kusa da ofishin gwamnatin Libiya, mai samun daurin gindin kasashen Yamma. Shaidu sun bayyana cewa, ko da shike babu tabbacin wadanda suka mutu ko suka jikkata, amma anga motoci da yawa wadanda harin ya tarwatsa. Wannan kuwa baya rasa nasaba da cewar an kai harin ne, kusa da man'yan ma'aikatu da suka hada da ma'aikatar harkokin waje da kuma ofishin shugaban kasar ta Libiya da MDD ta nada, wanda kuma ke fisktar adawa daga sauran mayakan kasar. Birnin Tiripoli dai yanzu yana hannun kungiyoyi mayaka daban-daban, inda ko wannensu ke neman ikon fada aji.