Hari kan ofisoshin yan sanda a Mogadishu | Labarai | DW | 29.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari kan ofisoshin yan sanda a Mogadishu

A kasar Somalia wasu yan bindiga sun kai hari kan ofisoshin yan sanda da dama a birnin Mogadishu inda suka halaka mutane 2,cikinsu da dan sanda daya.

Gwamnatin rikon kwarya ta Somalia tayi gargadin cewa mayakan islama da aka tarwatsa a watan daya gabata suna sake hadewa a birnin,ta kuma roki alummomin duniya da su aike da dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa kasar.

Firaminista Meles Zenawi na kasar Habasha wanda dakarunsa suka taimaka korar mayakan islama yace kashi daya bisa uku na sojojinsa zasu janye cikin makonni biyu masu zuwa.