1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari kan masallaci a Afganistan

October 8, 2010

Wani gwamna a Afganistan ya rasu sakamakon harin bam a wani masallacin Juma'a

https://p.dw.com/p/PZqA
Gwamnan lardin Kundus, Mohammed Omar wanda aka halaka a wani hari da aka kai kan wani masallacin Juma'a a arewacin AfganistanHoto: picture alliance/dpa

Rahotanni daban daban dake fitowa daga arewacin Afganistan na cewa mutane kimani 21 sun rigamu gidan gaskiya sakamakon harin bam da aka kan wani masallaci. Daga cikin waɗanda suka rasu a wannan harin da aka kai a birnin Talukan har da gwamnan lardin Kundus Mohammed Omar. Shi dai gwamnan ya kasance jagaba a jerin masu sukar lamirin sojojin sa kai na Taliban kuma yayi ta gargaɗi game da angizon da suke ƙara samu tare da yin kira da a ƙarfafa matakan soji kansu. Yana kuma adawa da duk wata tataunawar da mayaƙan Taliban. Shi dai gwamnan yana cikin masallaci lokacin Sallar Juma'a sanda aka kai harin. Al'amuran tsaro dai sai ƙara dagulewa suke yi a ƙasar ta Afganistan, inji Dari Assadullah Walwagi masanin harkokin tsaro.

"Wannan harin ya nuna a fili cewa har yanzu hukumomin leƙen asirin gwamnatin Afganistan da kuma ƙasashen da ke mara musu baya suna da rauni. Ba za su iya hana kai irin wannan harin da sojoji kaɗai ba, dole sai da taimakon hukumomin leƙen asiri."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu