Hari kan Kiristoci a Bagadaza | Siyasa | DW | 10.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hari kan Kiristoci a Bagadaza

Ƙasashen duniya na ci-gaba da yin tir da hare haren bama-bamai da ake kaiwa mabiya addinin Kirista a Iraqi

default

Babban fadan Katholika a Iraqi a ziyarar ganewa ido bayan harin da aka kai kan cocin Katholika a Bagadaza

Sun bayyana hare haren da cewa wani yunƙuri ne na mayar da hannun agogo baya a ƙoƙarin ɗinke ɓaraka tsakanin al'ummomin ƙasar.

Kwanaki 10 bayan mummunan harin da aka kai kan wani cocin Katholika a Bagadaza, har yanzu ana ci gaba da kai hare-hare kan Kiristocin Iraqi, inda a wannan Larabar aka sake kai wani harin da ya halaka mutane 10 sannan da dama suka samu raunuka a jerin hare hare a faɗin ƙasar ta Iraqi. Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ya kaɗu kuma yayi tir da hare haren da sojojin sa kai ke kaiwa Kiristoci da Musulmi a Iraqi. Jakadan Faransa a Majalisar Gerard Araud ya bayyana harin da cewa wani yunƙuri ne da nufin share al'umar Kiristan Iraqi, da ke kan gaba wajen girke demukuraɗiyya a ƙasar.

A safiyar jiya aka sake kai harin bama-bamai 14 a wata unguwar Kirsitoci dake Bagadaza da ya halaka aƙalla mutane uku sannan kimanin 30 suka samu raunuka. An ƙiyasce cewa gamaiyar Kiristoci a birnin na Bagadaza ta yi asarar kashi biyu bisa uku na ya'yanta waɗanda suka tsere zuwa ƙasashen ƙetare ko tudun mun tsira a yankunan Ƙurdawa kamar yadda wannan ɗalibi mai suna Nawar ya nunar.

"A unguwa kamar Dora inda bama-baman na yanzu suka fashe, ana fatattakar mutane ne don suna kiristoci."

Gwamnatin Iraqi dai ta yi suka ga ƙaurar da Kiristocin ke yi inda ta ɗora laifin ga ƙasashen yamma dake ƙarfafa wa Kiristocin guiwa da su fice. Kawo yanzu Faransa ta karɓi mutane 34 da suka samu rauni lokacin garkuwar da aka yi da masu ibada a cikin wani coci kuma tana da niyar ɗaukar ƙarin Kiristocin. A nan Jamus ma da yawa daga cikin 'yan gudun hijirar Iraqi 2500, Kiristoci ne.

Sabri al- Maqdissi fada ne a yankin Ƙurdawa na Erbil, ya ce ƙaurar babbar asara ce ga Iraqi. Tun bayan kifar da gwamnatin Saddam Hussein yawan Kiristoci a Iraqi ya ragu da kimanin kashi 50 cikin 100 ya zuwa dubu 500.

"A Bagadaza yawansu ya kai dubu 200 kuma har yanzu suna ci-gaba

da ƙaura. Dole ne gwamnati ta kula da wannan hali domin mutane ne da aka kashe kuɗin ƙasa aka ba su ilimi. Wata asarar ce ta tattalin arziki. Ba wai Kiristoci ne kaɗai ke fuskantar wannan matsala ba, hakan ya shafi sauran 'yan ƙasar."

Hukumomi a Iraqi dai ba za su iya samar da wani tsaro ga al'uma ba, musamman saboda har yanzu an kasa kafa wata gwamnatin ƙawance watanni takwas bayan zaɓe a ƙasar.

Mawallafa: Ulrich Leidholdt/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Ahmad Tijani Lawal