Hari kan Islamiya a Thailand | Labarai | DW | 18.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari kan Islamiya a Thailand

Daruruwan musulmi ne suke gudanar da zanga zanga a wani kauye na kasar Thailand suna masu Allah wadai da harinda aka kai kan wata makarantar islamiya inda wasu dalibai uku suka rasa rayukansu wasu kuma 7 suka samu rauni.

Masu zanga zangar sun hallara a harabar makarantar dauke da gawarwakin wadannan dalibai suna masu cinna wuta kann wani ginin gwamnati da kuma wata makaranta mallakar gwamnati.

Yan sandan kasar sun dora laifin harin kann yan gwagwarmaya na islama a kasar,zargi da tuni mazauna kauyen suka karyata.

Komishinan yan sanda na yankin kanar Thammasak yace a daren jiya asabar ne aka kai hari kann dakin kwanar daliban inda kimanin samari 75 suke barci.