Hari akan maaikatan hukumar kula da yan gudun hijira ta mdd a sudan | Labarai | DW | 16.03.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari akan maaikatan hukumar kula da yan gudun hijira ta mdd a sudan

SUDAN

Wasu yan bindiga dadi sun kai hari a gidajen maaikatan hukumar kula da yan gudun hijira ta MDd a kudancin Sudan,inda suka kashe mai tsaron wurin tare da raunana wani maaikacin sufuri dan kasar Iraki.Rahotanni daga yankin dai na nuni dacewa a yanzu haka dai am kawar da mutane biyun daga yankin,wadanda ke kann hanyarsu ta zuwa birnin Nairobin kasar Kenya.Kakakin hukumar kula da yan gudun hijiran Helene Caux ta bayyana cewa suna laakari da wannan hali da maaikatan ke ciki,tare da nazarin yiwuwar kaurar dasu daga kudancin sudan din.Sanarwar hukumar dai tace a harin na daren jiya,an bindige Dan Irakin a ciki,ayayinda aka harbi mai tsaron wurin a kafa.Kakakin ta kara dacewa an bindige daya daga cikin masu kai harin har lahira,ayayinda gudan yake tsare a kurkukun Yei.

 • Kwanan wata 16.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7O
 • Kwanan wata 16.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7O