Hari a wurin jana'iza ya hallaka mutane a Kabul
June 3, 2017Talla
Wasu rahotanni na cewar mutane 20 ne suka rasu a Afghanistan bayan da wasu jerin bama-bamai uku suka tashi a wannan rana ta Asabar kusa da masu jana'iza ta wani da ya rasa ransa bayan taho mu gama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga a ranar Juma'a. Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin jami'an tsaro da ma wasu da suka sheda yadda klamarin ya faru.
Wani da ya ga yadda abun ya faru da bai so a bayyana sunanasa ya ce mutane 12 ne yayin da wata kafar yada labaran talabijin a kasar ta Afghanistan Tolo News kuma ke cewa mutane 18 ne suka rasu.