1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari a wata cibiyar shaƙatawa ta ƙasar France

A ƙasar France, wasu mutane ɗauke da makamai, sun kai hari ga wata cibiyar yawan shaƙatawa, dake kussa da Ajaccio.

Wannan hari, ya yi kaccakaca, da gidaje 5, dake kewayen wurin,saidai ba a samu assara rayuka ba, kasancewar gidan na rufe, a lokacin da ta´adin, ya wakana.

Mai gadin wannan gida da maharan su ka ɗaure, ya sanar da jami´an tsaro cewa, ƙungiyar FLNC, mai kishin yankin Corse, na ƙasar France,ke da alhakin kai wannan hari.

Cemma, ranar 24 ga watan Janairu, na shekara ta 2005, wani hari ya rutsa da wannan cibiya.