Hari a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
May 2, 2018Talla
Kafar yada labarai ta Vatican da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar ta ruwaito cewa, harin da aka kai a wata cocin mabiya darikar katolika mai suna Church of Fatima an kai shi ne da gurneti kana harin na masallaci da asibitoci aka kai shi da abubuwa masu fashewa. Rahotanni sun nunar da cewa mutane 100 ne suka jikkata sakamakon wannan hari. Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai na zaman guda daga kasashen Afirka da ke fama da tashe-tashen hankula da ke da nasaba da siyasa da addini da kuma kabilanci.