Hari a Darfur | Labarai | DW | 10.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari a Darfur

Masu lura da tsaro a lardin Darfur din kasar Sudan daga kungiyar gammayar Afrika,sun sanar dacewa wasu yan bindiga dadi sun kashe fararen hula 22 tare da raunana wasu 10,a kusa da kann iyakokin sudan da Chadi.An danganta wannan harin da mayakan larabawa dake daurin gindin gwamnatin Khartum,hari daya zo adai lokacin da ake gudanar da zagayowar shekara adangane da halinda lardin Darfur ke ciki,kana da gudanar da gamgamin bukatar kawo karshen cigaba da fyade da akeyiwa mata da yammata a yankin.Kungiyoyin mata daga sassa daban daban na duniya dai sunyi kira da akawo karshen wannan cin zarafin da matan Darfur ke cigaba da kasancewa ciki,sakamakon barkewan fada.Rahotanni na zargin dakarun sojin gwamnatin Sudan da aikata wannan cin zarafi wa matan a Darfur.