Hari a Bagadaza ya kashe yan majalisa biyu | Labarai | DW | 12.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari a Bagadaza ya kashe yan majalisa biyu

A kai hari a harabar majalisar dokokin kasar Iraki dake birnin Bagadaza,wanda ya kashe yan majalisa biyu tare da raunana wasu 10.Rahotanni daga bagadazan na nuni dacewa,an kai harin ne a cikin wurin cin abinci dake harabar majalisar dokokin , adaidai lokacin da yan majalisar ke cin abincin rana.Ginin majalisar dokokin Irakin dai na cikin yankin nan na Green Zone,dake birnin na Bagadaza.Da safiyar yau nedai wani dan kunar bakin wake ya tayar da bomb dake cikin motarsa akan gadar kogin Tigris dake fadar gwamnatin kasar,harin daya ritsa da rayukan mutane 10.Har yanzu dai jamian yansanda cikin jiragen ruwa na cigaba da neman wadanda harin ya ritsa dasu cikin kogi ,sakamakon rushewan gadan.