Hare-harena Irak
October 9, 2006Talla
A ƙasar Iraki an ci gaba da bata kashi, tsakanin sojojin Amurika, da yan yaƙin sunƙurun Schi´a.
Artabon da ya wakana jiya, a yankin Diouaniya, ya hadasa mutuwar a ƙalla mutane 20.
Rahotani daga ƙasar, sun ce sojojin Amurika, sun fuskanci wannan sabuwar turjewa, daga magoya bayan Limamin yan Schi´an nan, mai faɗa a ji, Mokhtada Sadr, wanda su ka zargi sojojin Amurika, da karya alkawarin da su ka ɗauka na ba za su shiga ba a Diouaniya.
Sannan a sassa daban-daban na ƙasar, kamar yada a ka riga a ka saba, an ci gaba da kai hare-haren kunar baƙin wake, wanda su ka hadasa mutuwar sojojin Amurika 29 a tsukin sati guda.
A ɗaya wajen kuma yau ne za a ka koma shari´ar tsofan shugaban ƙasa Sadam Hussain a birnin Bagadaza.