Hare-haren tawaye a yankin Darfur | Labarai | DW | 04.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren tawaye a yankin Darfur

A ƙalla mutane 12 su ka rasa rayuka, da su ka haɗa da yaya mata guda 2 a cikin sabin hare haren,da yan tawayen Darfur su ka kai, a Hamrat al-Cheick da ke jihar Kordofan.

Hare haren, da su ka wakana a ranar jiya litinin na matsayin wata sabuwar alama, mai nuna cewar tsugune ba ta ƙare ba, a yankin duk kuwa, da yarjejeniyar zaman lahia, da aka rattawa hannu, a birnin Abuja na Taraya Nigeria, tsakanin yan tawaye da dakarun gwamnati.

A halin da ake ciki, rahotani daga yankin da abun ya faru, sun ce mutane sun shiga gudun hijira, domin tsira da rayukan su.

Kuma sojojin gwamnatin sun shiga farautar ƙungiyar tawaye ta JEM, da aka ɗorawa alhakin kai harin.

An yi ɓarin wuta na tsawan kimanin sa´o´i 2, tsakanin ɓangarorin 2, wanda ya jawo mutuwar yan sanda 8, da assara gidaje masu yawa.

Kumqa sanarwa daga fadar mulki, dake Khartum, ta ce dakarun gwamnati, sun sami nasara furgadar yan tawayen daga Hamrat al-Cheick.

Wannan hari ya wakaka kwana ɗaya rak, bayan da ƙungiyar taraya Afrika, ta mince da ƙara wa´adin rundunra AU, dake shiga tsakanin a yankin Darfur.