1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru na fuskantar hare-haren kunar bakin wake

Mahamadou Danda/LMJJuly 27, 2015

Bayan harin kunar bakin wake a Kamaru, mahukuntan kasar sun bayar da umurnin rufe Masallatai da makarantun Islamiya a arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/1G5Iv
Tsaurara matakan tsaro a Kamaru
Tsaurara matakan tsaro a KamaruHoto: Reinnier Kaze/AFP/Getty Images

Wannan matakin dai da hukumomin suka dauka ya biyo bayan harin kunar bakin wake da aka kai a arewacin kasar a karshen mako wanda ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane akalla 60 tare da raunata wasu masu yawa. Rahotanni sun nunar da cewa baya ga Masallatan da Makarantu da hukomomin Kamarun suka bayar da umurnin rufewa sun ma bayar da umurnin hana yara kanana yin bara a kan tituna. Mahukuntan kasar na Kamaru sun ce sun dauki matakin hana yara kanana bara ne kasancewar a yanzu ana amfani da su wajen kai hare-haren kunar bakin wake. Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin harin kunar bakin waken na karshen mako da aka kai a garin Maroua, sai dai mahukuntan kasar Kamarun na dora alhakinsa a kan kungiyar Boko Haram da ta addabi makwabciyar kasa Tarayyar Najeriya. Al'ummar jihar Arewa Mai Nisa da lamarin y ashafa dai sun nuna amincewarsu kan matakan da gwamnatin ke dauka domin tabbatar da tsaro.