Hare Haren ta´addanci a Indiya | Siyasa | DW | 28.07.2008
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hare Haren ta´addanci a Indiya

Harin wani makarci da nufin dagula al´amura a Indiya, inji gwamnati.

default

Wata bas da aka kaiwa hari a Ahmedabad


Bayan ta yi Allah wadai da hare haren da aka kai a Indiya a ƙarshen mako wanda ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane 49, ƙungiyar tarayyar Turai ta yi alƙawarin bawa ƙasar taimako a yaƙin da ta ke yi da ´yan ta´adda.


Ƙasashen duniya sun yi tir da fashewar bama-baman kimanin 16 a cikin kasuwanni, unguwanni, motocin haya da kuma asibitoci a birnin Ahmedabad da ke cikin jihar Gujarat da cewa wani makirci ne da nufin haddasa ruɗami a ƙasar ta Indiya. Hukumomin Indiya sun zargi wasu da suka kira marasa kishin ƙasa da ƙoƙarin janyo fargaba a tsakanin al´umar ƙasar. An jiyo ministan cikin gidan Indiya Shivraj Patil yana cewa hare haren na birnin Ahmedabad da ya halaka mutane 49 sannan wasu 160 suka samu raunuka wani ɓangare ne na wannan maƙarkashiya.


Ya ce "Ba mu da wata shakka ko ta misƙala zarratin cewa gwamnatin jihar za ta taimakawa waɗanda hare hare suka rutsa da su. Ita ma gwamnatin Indiya za ta taimaka matuƙa."


Ana cikin zullumi a birnin mai al´ummomi daban daban, inda a shekara ta 2002 mutane sama da dubu ɗaya ɗaukaci musulmi aka kashe a wata mummunar arangama tsakanin ´yan Hindu da Musulmi.


Jim kaɗan bayan da shugabanni suka yi kira da a kwantar da hakula, dakarun gwamnati sun kafa sansanoni a faɗin birni a wani mataki na tsaurara matakan tsaro don hana ´yan Hindu ɗaukar fansa kan Musulmi.


Rahotanni sun  yi nuni da cewa hukumomin tsaron Indiya sun kame mutane 30 da ake zargi da hannu a wannan ta´asa, wadda wata ƙungiyar musulmi da ke kiran kanta Mujahiedeen a Indiya wadda ba sananniya ba ce ta yi iƙirarin kaiwa. Jami´an tsaro dai na zargin ƙungiyar da alaƙa da ƙungiyar Lashkar e-Toiba ta ´yan takife a Pakistan, wadda ta yi iƙirarin kai harin watan Mayu a birnin Jaipur da ya halaka mutane 65.


Kakakin rundunar ´yan sanda a birnin Ahmedabad Raman Srivathasa ya yi kira ga mazauna birnin da su taimakawa ´yan sanda wajen zaƙulo waɗanda ke da hannu a wannan ta´asa.


Ya ce "Muna buƙatar haɗin kanku domin mu gano ɓata gari da kuma baƙin da ba mu amince da su ba da a halin yanzu suke tsakaninmu."


Yanzu haka dai ana cikin shirin ko takwana yayin da aka tsaurara matakan tsaro a dukkan manyan biranen ƙasar musamman a wuraren ibada, ofisoshin gwamnati, filayen jiragen sama da kuma tashoshin jiragen ƙasa.


A yau Litinin Firaminista Manmohan Singh da wasu shugabannin Indiya za su kai ziyarar ganewa ido a birnin Ahmedabad da ke yammacin ƙasar.

 • Kwanan wata 28.07.2008
 • Mawallafi Matthay, Sabina / New Delhi (NDR)
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/ElEn
 • Kwanan wata 28.07.2008
 • Mawallafi Matthay, Sabina / New Delhi (NDR)
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/ElEn