1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren ta´adanci a Sinai

April 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0k

Ƙasashen dunia na ci gaba da yin Allah wadai ga hare haren ta´adancin da su ka wakana jiya, a Masar.

Wasu yan ƙunar baƙin wake ne, su ka kai wannan tagwayen hare hare, a Dahab, da ke yankin Sinai, inda a nan take, mutane fiye da 20, su ka rasa rayuka, a yayin da dama su ka ji mumunan raunuka.

Opishin ministan cikin kigida, ya bayyana cewar akwai daga wanda su ka mutu, 3 yan ƙasashe ketare, da su ka haɗa da wani jariri na ƙasar Jamus.

Hare haren, sun yi setin wasu gidajen ci abinci guda 2, da kuma wani babban shago makil da mutane, a Dahab, da ke tazara kilomita 530 ,da birnin Alƙahira.

Shugaban ƙasar Masar Osni Mubarack, ya alkawarta cewa, jami´an tsaro za su farautar masu alhakin kitsa wannan ɗanyan aiki, sannan kotu ta zartas da hukunci ,da ya dace da su.

Tunni, Kasashen Turai, Amurika da Majalisar Dinkin Dunia, sun yi hurucin a game da wannan sabin hare haren ta´adanci, wanda ke kara nuna wajibcin matsa lamba, da gama karfi,a yaƙi da ta´adancin inji shugaba Bush na Amurika.