Hare-haren ta´adanci a ƙasar Irak
April 12, 2006Talla
A ƙasar Iraki, kamar yadda a ka saba kullum, yan kunar baƙin wake, na ci gaba da kai hare hare, a Bagadaza, da sauran birane na wannan ƙasa.
Da sanhin sahiyar yau, mutane 8, su ka rasa rayuka a wasu tagwayen hare hare, a arewancin Bagadaza.
Ire iren wannan hari, ya wakana a birane, kamar su Tal Afar da Kales.
A ɓangaren sojojin Amurika kuwa, rahotani sun bayyana cewar su 5, su ka sheƙa lahira, daga ranar lahadi zuwa yau.
Daga ɓarkewar yaƙin Iraki, a shekara ta 2003, zuwa yanzu, sojojin Amurika 2.360 su ka kwanta dama.
Ta fannin siyasa kuwa, har yanzu, a na ta kai ruwa rana, a game da girka sabuwar gwamnati.