Hare-haren sojojin ƙawance a Afghanistan | Labarai | DW | 18.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren sojojin ƙawance a Afghanistan

Sojojin ƙawace a ƙasar Afghanistan, sun kai hare ga wata madarsa da kuma massalaci,a yankin kudancin kasar, tare da hallaka ƙananan yara 7.

Sojojin ƙasa da ƙasa na zargin wannan wurare da kasancewa maɓoyar yan takifen Taliban, da su ke nema ruwa jallo.

Wannan hare-hare a wurare masu tsarki, sun hadasa mutuƙar ɓacin rai daga al´ummomin ƙasar Afghanistan, wanda cemma ke ciki-ciki da dakarun Amurika, bayan kissan gillar da su ka yi wa fara hulla a watan da ya gabata.

A wani mataki na maida martani, mayaƙan taliban sun kai hari ga wata tawagar sojojin Nowe, a yayin da ta ke sintiri a yankin Faryab, saidai bau cikkaken bayani, a game da yawan mutanen da su ka rasa rayuka, ko su ka jikata a sakamakon ɓarin wutar da ta haɗa ɓangarorin 2.

Ƙungiyar tsaro ta NATO ta sha alwashin murƙushe bornin yan tawayen Taliban a ƙasar Afghanistan, to saiodai ya zuwa yanzu, ta na fuskantar turjewar bil haƙi da gaskiya, daga wannan ƙungiya mai tsatsauran ra´ayin addinin islama.