1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren kunar bakin wake a Najeriya

Abdourahamane Hassane
September 18, 2017

Wasu jerin hare-hare na kunar bakin wake guda uku jere sun yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 15 a lokacin aikin raraba abinci a cikin wani sasanin 'yan gudun hijira da ke a arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/2kEDH
Nigeria Stadt Borno State
Hoto: picture-alliance/dpa/Stringer

Hare-haren wadanda aka kai da misalin karfe 11 na safiyar Litinin a garin Mashalari a yankin Konduga mai nisan kilomita 30 daga Maiduguri a yayin da 'yan gudun hijira ke layin karbar abinci ya kuma  jikkata mutane kusan 43. Ana dai zargi 'yan kungiyar Boko haram da kai hare-haren.