Hare-haren kunar bakin wake a kasar Jordan | Labarai | DW | 10.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren kunar bakin wake a kasar Jordan

A daren jiya, yan kunar bakin wake, sun kai hare hare a hotel hotel 3, da ke Amman babban birnin Kasar Jordan.

Yazuwa yanzu, mutane a kalla, 57 su ka rasa rayuka, a cikin wannan hari, a yayin da fiye da 300 su ka ji mumunan raunuka.

Wannan ayyukan ta´adanci sun abku, a lokacin da Sarki Abdallah na Jordan, ke cikin bullaguro.

Kasashe da kungiyoyi daban daban na dunia, na ci gaba da Allah wadai ga hare haren.

Komitin sulhu na Majalisar Dinkin dunia, ya kudurci shirya taro na mussamman, nan gaba a yau, domin tantana batun.

Duk da cewa, har yanzu babu wanda su ka dauki alhakin harin, a na zargin kungiyar Alka´ida, reshen Abu musab Alzarqawi, dan assulin Jordan.

Sakataran majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan ,da a yau ne ya shirya kai ziyara a Jordan ya soke ziyara ta sa.

A fadin Birnin na Amman, an tsatsawra matakan tsaro, kuma hukumomi sun bayanna rufe iyakokin Jordan har zuwa wani lokaci da ba a kayyade ba, sun kuma umurci jama´a, ta shiga zaman makoki yau, a kasar baki daya.