Hare haren kunar bakin wake a Iraki
November 2, 2005Talla
A kasar Iraki kamar yadda a ka saba kullum, yan kunar bakin wake na ci gaba da kai hare hare babu kakkabtawa.
Wani harin da su ka kai yau, ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 yan shi´a a massalacin Mussayeb dake kudanci birnin Bagadatza, da kuma rauna mutane fiye da 50.
A watan Juli da ya wuce ,wani hari makamancin wannan ya rutsa da birnin Mussayeb, inda ya jawo murtuwar mutane kussan 100.
A bangaren sojojin Amurika kuwa, 5 sun rasa rayukan su tsakanin jiya da yau laraba.