Hare-haren kunar bakin wake a Chadi
December 5, 2015Talla
Shaidun gani da ido sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai na AP cewar baya ga wanda suka rasu din, wasu da suka kai 90 sun samu raunuka, wasunsu ma munana.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda Chadi din a wajen da wannan hari ya wakana ya ce wasu mata ne uku dauke da bama-bamai suka kai harin.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dau alhakin kai wannan harin, sai dai kungiyar nan ta Boko Haram ta kai jerin hare-hare a Chadi din don ko a watan jiya ma sai da wata 'yar kunar bakin wake ta hallaka mutane 3 a wani kauye dab da tafkin Chadi.