Hare-haren Isra´ila a zirin Gaza
August 31, 2006Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, yayi kira ga ƙasashen dunia, da su tsawatawa Isra´ila, ta dakatar da kai hare hare, zuwa yankunan Palestinu.
Abbas ya jaddada wannan kira bayan da rundunar Isra´ila ta hallaka wasu fara hulla guda 9 da basu san hawa ba balle sauka.
A ɗaya hannun kuma, ya gayyaci yan yaƙin sunƙurun Palestinu, su daina harba rokoki daga zirin Gaza, zuwa Isra´ila, domin a cewar sa, hakan ya zama aibu, ga zaman lahia da kwanciyar hankali a cikin kasa.
Saidai ɓangarorin 2, sun yi buruss da wannan kira, domin ko a sahiyar yau, Isra´ila ta kai wani samame a yankin Naplouse, wanda ya yi sanadiyar mutuwar Fadi Qafishey shugaba dakarun Al-Aqsa.
A dangane da halin da ake ciki a zirin Gaza, mataimakin sakaren hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Dunia, Jean Egeland, ya ja hankalin Majalisar, bisa mahimancin duba wannan matsala da idon basira.