1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Isra´ila a zirin Gaza

November 2, 2006
https://p.dw.com/p/BudW

Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, ya gana da mataimakin sakataren harakokin wajen Amurika, mai kulla da yankin gabas ta tsakiya David Welch.

Mahamud Abbas ya bukaci gwamnatin Amurika ta tsawatawa Isra´ila, domin ta daina kai hare hare, a zirin Gaza.

Kakakin gwamnati fadar shugaba Abbas, ya yi tur da Allah da wannan hare-hare, wanda ke ƙara mayar da hannun agogo baya, a yunƙuri samar da zaman lahia a yankin gahas ta tsakiya.

Shima ministan tsaron Jamus Franz Josef Yung, a halin yan zu na cikin rangadi a wannan yanki, inda Jamus ke sa ran bada gudummuwa, wajen batun zaman lahia.

Bayan Libanon da Isra´ila, Yung zai gana da hukumomin Palestinu.

A game da matsayin Jamus, a kann harakokin tabatar da tsaro yan siyasar kasar na adawa da amsu mulki su cimma matsaya guda,a gaem da rawar da Jamus ke takawa, inji kakakin jam´iyar the Greens mai adawa, Winfried Nachtwei.