1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Iran kan ƙurdawan Irak

May 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bv00

Kakakin jam´iyar ƙurdawa ta PKK, dake arewancin Irak, ya bayanawa manema labarai cewar, kwanaki 2 babu ƙaƙƙabtawa, rundunar tsaron Iran, na amen wuta ga wannan yanki.

Tsakanin jioya lahadi da yau litinin ƙurdawa sun yi asara mai tarin yawa, a sanadiyar wannan ɓarin wuta.

A halin da ake ciki, mutane da dama, sun shiga halin gudun hijira, inji Aref Rushdie.

Kakakin PKK, na zargin Turquia da hannu a cikin wannan hare –hare, da Iran ke kaiwa yankin.

A nasa ɓangare, ministan harakokin tsaro na ƙasar Irak, ya zargi hukumomin Iran, da taka dokokin ƙasa da ƙasa, ta hanyar kai hari ga al´ummomin Irak, a cikin wannan ƙasa.