1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Dakarun Turkiyya a Arewacin Iraki

Tijani LawalFebruary 27, 2008

ƙokarin ƙasashe wajen ganin cewar Turkiyya ta janye Dakarun ta daga arewacin Iraki

https://p.dw.com/p/DEYi
Dakarun Turkiyya kan Iyakar Iraki.Hoto: AP

Gwamnatin tsakiya a kasar Iraki da kungiyar tarayyar turai da kuma Amurka na bakin kokarinsu wajen matsanta wa Turkiyya da ta sanya wani takamaiman wa'adi na janye sojojinta daga arewacin Iraki. To sai dai kuma har yanzun hakansu bai cimma ruwa ba, saboda a jiya laraba dinnan ne fadar mulki ta Ankara ta fito fili tayi fatali da wannan bukata. Fadan da ake gwabzawa a yankin iyaka ya jefa Kurdawan Turkiyya cikin mawuyacin hali na rayuwa..

A dai halin da ake ciki yanzun kaka ta fara karatowa a yankin kudu-maso-gabacin Turkiyya, kuma manoma sun himmatu a bakin aikinsu. Yawa-yawancin mazauna yankin na lardin Mardin Kurdawa ne makiyaya da manoma, wadanda a cikin shekaru 20 da suka wuce suka kasa samun ikon ayyukansu na noma da kiwo sakamakon fada tsakanin dakarun kungiyar fafutukar neman 'yancin kan Kurdawa na PKK mai ra'ayin gurguzu da askarawan Turkiyya, kamar yadda aka ji daga bakin wasu matasa su biyu dake kiwon tumakinsu. Wadannan matasa suka ce tsawon rayuwarsu ba abin da suka shaidar illa yaki da talauci. Daya daga cikinsu mai suna Aziz ya kara da cewar:

"Ban taba shiga ajin makaranta ba a sakamakon haka tilas na hakura da wannan aiki, ina so ko bana so."


Babban abin da mazauna yankin ke buri shi ne a giggina musu masana'antu ta yadda zasu samu wata kyakkyawar kafa ta neman kudaden shiga, amma a sakamakon rikicin na PKK ba wani dan kasuwar dake sha'awar zuba jari a yankin kudu-maso-yammacin Turkiyya. A wani dan karamin garin da ake kira Cizre dake gabar kogin Tigris a iyaka da Iraki, mutane sun dogara ne kacokam akan ciniki da arewacin Irakin don samun kudaden shiga. A can baya dai kome na tafiya salin-alin, kamar yadda aka ji daga bakin wani direban babbar mota Yakub Demirtas dake da shekaru 22 da haifuwa. Amma a cikin kiftawa da Bisimillah sai kome ya canza ya dauki wani sabon salo mai munin gaske tun bayan kutsawar sojojin Turkiyya a yankin. Yakub Demirtas ya kara da cewar:


"A sakamakon kutsen sojan Turkiyya muka shiga wani mawuyacin hali na rayuwa, saboda an rufe daya iyakar dake tsakanin Iraki da Turkiyya, kuma mutane sai zaman kashe wando suke yi ba su da aikin yi. Idan kuma an rufe daya iyakar, wadda ita ce mafi girma to kuwa zamu gwammace kida da karatu."


Duk dai wanda yayi rangadin wannan yanki zai ga irin radadin wahala da jama'a ke fuskanta, ba aikin yi ballantana a samu abin sakawa bakin salati. Maddin kuwa aka ci gaba da fama da wannan mawuyacin hali ba za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.