1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren bom a Algiers

April 12, 2007

Shin Aljeriya na fuskantar barazanar sake komawa wani sabon yakin basasa ne irin shigen na shekarun 1990.

https://p.dw.com/p/Btvo
Tashin bamabamai a Aljeriya
Tashin bamabamai a AljeriyaHoto: picture alliance/dpa

Tun bayan hare-haren 11 ga watan satumba danganta duk wani hari na ta’addanci da kungiyar al-ka’ida ta Osma Bin Laden ta zama al’ada. A hakika kuwa ana sanya wa masu alhakin ire-iren wadannan hare-hare wannan tambari ne saboda rufa-rufa a game da gazawar da ake fama da ita wajen tinkarar matsalar dake akwai. An dai mayar da kungiyar ta al-ka’ida tamkar wani kamfani ne na ‘yan ta’adda da kowa-da-kowa ke iya sayen hannun jari a cikinsa, duk kuwa da cewar tuni kungiyar ta al-ka’ida ta tarwatse ba ta da wani tasiri a ayyukan ta’adda na kasa da kasa, illa kawai wasu dake amfani da wannan suna domin tafiyar da kazamin aikinsu. An lura da cewar tun a farkon wannan shekarar wasu kungiyoyi masu tsananin kishin addinin islama ke bin wannan manufa a yankin Maghreb na arewacin Afurka. Kungiyar ‘yan mazan jiya ta salafi a kasar Aljeriya GSPC a takaice a hadin kai da kawayxenta na kasashen Moroko da Mauritaniya da Tunesiya suka lakaba wa kansu sunan kungiyar al-Ka’ida mai fafutukar tabbatar da musulunci a yankin Maghreb. Dukkan kungiyoyin sun lashi takobin saka kafar wando daya da gwamnatocin kasashensu, domin maye gurbinsu da gwamnatoci masu biyayya ga shari’ar musulunci a harkokin rayuwa ta yau da kullum. An taba fuskantar wannan matsala a cikin shekarun 1990 lokacin da kungiyoyi daban-daban dake ikirarin kishin islama suka shiga zub da jini domin kifar da gwamnatin Aljeriya bayan da aka soke nasarar da wata kungiya ta musulmi ta samu a zaben kasar da aka gudanar a shekara ta 1992. Daga cikin dakarun da suka shiga aka rika gwagwarmaya da su har da tsaffin mayakan mujahideen na kasar Afghanistan. Amma fa ko da yake Osama Bin Laden da al-Ka’ida sun yi tasiri a Afghanistan, amma akwai banbancin manufofi tsakanin Aljeriya da kasar ta Afghanistan. Domin kuwa ita Aljeriya musabbabin rikicinta shi ne mawuyacin hali na talauci da tabarbarewar al’amuran rayuwa da rashin hangen wata kyakkyawar makoma, musamman tsakanin matasa hade da mulki na danniya da kama kariya tare da taimakon kasashen Faransa da Amurka. Kuma ko da yake al’umar Aljeriya ba sa fatan ganin kasarsu ta sake fadawa cikin mawuyacin hali na yakin basasa, amma fa suna begen walwala da kyautata makomar rayuwarsu, matsawar hakan bata samu ba to kuwa masu zazzafan ra’ayin Islama zasu ci gaba da samun goyan baya, wadanda ba kawai haushin shuagabanninsu suke ji ba har ma da masu goya musu baya a ketaren tekun baha-rum da tsallaken tekun atlantika.